Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

KAROTA da Kotu : An dakatar da sauraran karar Baffa Babba kan Na’urar Tracker

Published

on

Babbar Kotun jihar Kano mai lamba bakwai karkashin jagorancin Justice Usman Na Abba ta bada umarnin dakatar da saurarar karar da aka shigar gaban Kotun Majistiri mai lamba 12 wanda wani direban Adaidaita sahu ya shigar gabanta yana kalubalantar shugaban hukumar Karota Baffa babba Dan agundi kan zargin na’urar Tracker.

Tunda fari dai kotun Majistiri karkashin mai shari’a Muhammad Jibril ta sanya ranar yau 19 ga watan Oktoban da muke ciki a matsayin ranar da shugaban hukumar Karota Baffa Babba Dan Agundi zai gurfana a gabanta domin cigaba da sauraron shari’ar.

Sai dai a zaman Kotun na yau mai shari’a Muhammad Jibril ya karanta odar dakatarda sauraron shari’ar da Babbar Kotun ta bayar wanda ta sanya ranar ashirin da shida ga watan da muke ciki a matsayin ranar da zata cigaba da sauraron shari’ar.

Batista Abba Hakima Fagge shine Lauyan mai shigar da kara yace zasu rubutawa Babbar Kotun amsa domin baiwa Kotun Majistirin damar cigaba da sauraron karar da suka shigar gabanta.

Ana nasa bangaren Lauyan Baffa Babba Dan Agundi Batista Muttawakkil Ishak yace tun da farko an shigar da karar ne ba bisa ka’idaba wanda hakan yasa suka garzaya gaban Babbar Kotun domin ta dakatar da cigaba da sauraron karar a gabanta.

KAROTA ta kai sumame Gandun Albasa

Ba ni da wani shiri na musanya wasu jami’an KAROTA – Inji Baffa Babba

Wakilin mu na Kotu da ‘yan sanda Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito cewa Babbar Kotun ta Kano karkashin Justice Usman Na Abba ta sanya ranar ashirin da shida ga watan da muke ciki domin cigaba da sauraron karar da masu kara suka shigar gabanta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!