Connect with us

Labarai

Yanzu -yanzu: kwale-kwele ya kife da Ɗaliban islamiyya a Kano

Published

on

Wani kwale-kwele ɗauke da ɗaliban makarantar Islamiyya ya nutse a ƙaramar hukumar Ɓagwai.

lamarin ya haifar da mutuwar ɗalibai 10 yayin da sama da ɗalibai 30 suka ɓace a ruwan.

Wani shaidar gani da ido ya tabbatarwa da Freedom Radio cewa, sama da ɗalibai 24 an samu nasarar ceto su da yammacin ranar Talata.

Tun da fari dai an gano gawarwakin mutane 10 da suke shawagi a saman ruwan da ke madatsar ruwa ta Bagwai a karamar hukumar Bagwai a jihar Kano.

Rahotanni sun ce jirgin na dauke ne da daliban Islamiyya daga kauyen Badau zuwa Bagwai domin bikin Mauludi.

Cikakken bayani zai zo daga baya

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!