Labarai
Yanzu-yanzu: Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya rasu

Rahotonni daga birnin Zazzau na cewa Allah ya yiwa Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris rasuwa.
Wakilin Freedom Radio Hassan Ibrahim Zariya ya ce, sarkin ya rasu ne a asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna a yau Lahadi.
Yanzu haka dai tuni al’ummar masarautar Zazzau suka shiga jimamin wannan rashi.
A ɗaya ɓangaren daya daga cikin ƴaƴan sarkin ya shaida wa wakilin Freedom Radio Kaduna Babangida Aliyu Abdullahi rasuwar inda ya ce nan ba da jimawa za a sanar da jana’izarsa.
Muna tafe da ci gaban wannan rahoto a nan gaba.
You must be logged in to post a comment Login