Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu-yanzu: Shugaban EFCC ya faɗi a fadar shugaban ƙasa

Published

on

Shugaban hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa EFCC Abdulrasheed Bawa ya yanke jiki ya faɗi a fadar shugaban ƙasa.

Bawa ya faɗi lokacin da ya ke tsaka da gudanar da jawabi a wajen gudanar da bikin ranar katin shaidar ɗan Ƙasa.

Yana magana ne game da wani mutum da hukumar ta kama a Ibadan ta jihar Oyo, inda aka kama shi da layukan waya 116.

Rahotanni sun bayyana cewa an lura Bawa ya daina magana kuma nan take ya yanke jiki ya faɗi.

Ministan Sadarwa da tattalin arzikin Dakta Isa Ali Pantami, da wasu manyan jami’ai ne suka taimaka masa wurin ɗaga shi, kuma tuni aka garzaya da shi asibiti daga fadar shugaban kasa da ke Abuja

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!