Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Yanzu yanzu: ‘Yan bindiga sun sako daliban kwalejin nazarin tsirrai da gandun daji ta Kaduna

Published

on

Rahotanni daga garin Kaduna na cewa daliban kwalejin nazarin tsirrai da gandun daji ta Afaka da ke jihar Kaduna sun shaki iskar ‘yanci.

 

Daya daga cikin wadanda suka kwato daliban shi ya shaidawa jaridar Daily Trust labarin da yammacin ranar laraba.

 

Ya ce kwamitin da fitaccen malamin addinin musuluncin nan da ke Kaduna Sheikh Abubakar Gumi ya ke jagoranta da gudunmawar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne ya jagoracin sakin daliban.

 

Daliban 27 dai suna cikin 37 da ‘yan bindiga suka sace watanni biyu da suka gaba.

 

Bayan da iyayen yara suka biya kudin fansa a kwanakin baya ‘yan bindigar sun saki goma daga cikinsu yayin da suka ci gaba da garkuwa da sauran 27

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!