Connect with us

Labarai

Ikon Allah: Wata mata ta haifi ‘ya’ya 9 rigis

Published

on

Rahotanni sun ce a ranar talata ne Halima Cisse – mai shekara 25 ta haifi jariran nata

 

Jariran dai sun kunshi mata biyar da maza huɗu a wani asibiti da ke kasar Morocco

 

Kamar yadda ministan lafiyan kasar ta Mali Fanta Siby ta fitar ta cikin wata sanarwa.

 

Tun farko dai an sa ran Ms Cisse za ta haifi ƴaƴa bakwai ne bisa ga hoton cikinta da aka ɗauka a Mali da Morocco wanda bai iya gano cewa akwai karin jarirai biyu ba a cikinta.

 

Dr Siby ta ce jariran da mahaifiyarsu na cikin “ƙoshin lafiya”. Ana kuma sa ran za su koma gida nan da wasu makwanni.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!