Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu-yanzu- Ƴan bindiga sun sako ɗaliban Tagina

Published

on

Ƴan bindiga sun sako ɗaliban islamiyya Salihu Tanko da ke garin Tagina a jihar Neja.

Shugaban ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja Alhaji Isma’il Musa Ɗan Modibbo ya tabbatar da kuɓutar su a zantawar sa da wakilin mu Nuruddeen Isyaku Daza.

Alhaji Isma’il Musa ya ce, an samu dukkanin ɗaliban, ba tare da rasa ko da guda ba.

Tun da fari, Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa, wata majiya daga jami’an tsaro ta shaida cewa ɗaliban sun kuɓuta a yammacin Alhamis din nan.

Idan za a iya tunawa sama da ɗaliban islmaiyyar 70 ne masu garkuwa da mutane suka sace a watan Yuni.

Rahotanni sun bayyana cewa, yanzu haka ɗaliban na kan hanyar su ta Kagara zuwa Minna daga Birnin Gwari, bayan shafe kwanaki 88 a hannun ƴan bindigar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!