Connect with us

Ƙetare

Yariman Saudiyya ya bukaci Trump ya ci gaba da kai hari a Iran

Published

on

Wani rahoto da jaridar New York Times ta fitar ya bayyana cewa yariman Saudiyya mai jiran gado, Mohammed bin Salman, na matsa wa shugaban Amurka Donald Trump da ya ci gaba da yakin da ake yi da Iran.

 

A cewar majiyoyi da jami’an Amurka suka tattauna da su, yariman ya bayyana yakin a matsayin “dama ta tarihi” domin sake fasalin siyasar Gabas ta Tsakiya, yana ganin hakan zai iya sauya daidaiton iko a yankin.

 

Rahotannin sun nuna cewa an samu irin wadannan matsin lamba ne ta hanyar tattaunawa kai tsaye ta waya tsakanin bangarorin biyu, yayin da rikicin yankin ke kara tsananta.

 

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin Iran da kawancen Amurka da Isra’ila ke ci gaba da fadada, duk da kokarin diflomasiyya daga wasu kasashe na shiga tsakani.

 

Tun kafin hakan ma, wasu rahotanni sun nuna cewa Saudiyya da Isra’ila sun taka rawa wajen rinjayar matakin farko na kai hare-hare kan Iran, duk da cewa Riyadh ta sha musanta irin wannan zargi a bainar jama’a.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!