Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan sanda sun kama mai damfarar matasa

Published

on

Rundunar “yan sandar jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Yunusa D. Ado wanda yake amfani da wata gidauniya mai suna “End poverty” yana karbar kudi a hannun marasa galihu da sunan zai nema musu aiki domin shi yana da alaka da bankin duniya hadi da Organization na NGO da suke bada tallafi ga matasa.

Majiya mai karfi ta nuna cewa Yunusa Danlami Ado yana amfani da matasa ne maza da mata a matsayin jami’ansa  domin suje su karbo masa kudi a wurin mutane sai dai bincike ya nuna cewa wadannan jami’an nashi sune suka kai karar shi ofishin jami’an ‘yan sanda da yake Bompai.

Yadda matashi ya rasa ransa a hannun ‘yan sanda

‘Yan yahoo sun damfari loba boy

‘Yan sanda sun cafke sojoji kan KAROTA

Tuni dai jami’an “yan sanda suka gurfanar da wannan matashi a gaban kotu bayan sun kamashi a inda kotun ta bada umarnin cewa a cigaba da tsare shi har lokacin da aka gano gaskiyar al’amari.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!