Coronavirus
Yau da Gobe: Waɗanda suka kamu da Korona a Najeriya sun haura dubu 152

Gwamnatin tarayya ta ce ya zuwa yanzu cutar Corona ta kama jimillar mutane 152,616 cikin su kuma guda 129,300 suka warke sai kuma guda 1,862 suka rasa ransu a dalilin cutar.
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ce ta bayyana hakan ta shafin ta na twitter, inda ta ce a sakamakon gwajin cutar na jiya Litinin ya nuna cewar cutar ta sake harbar karin mutane 542.
A nan Kano ma dai kamar yadda aka saba a kullum ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce an sami karin mutane 8 da suka kamu da cutar, cikin mutane 44 da aka yiwa gwajin cutar.
Sai dai hukumar ta ce karin mutum guda ya rasu a nan Kano sanadiyyar cutar.
You must be logged in to post a comment Login