Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Karin mutum 164 sun kamu da Corona a Najeriya

Published

on

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta ce an sami karin mutane 164 da ke dauke da cutar Covid-19 a jiya Litinin.

Hukumar ta tabbatar da hakan ne ta shafin ta na Twitter kamar yadda ta saba, inda tace ya zuwa yanzu yawan wadanda cutar ta kama ya kai dubu 60,430 cikin su kuma dubu 51,943 sun warke sai kuma guda dubu 1,115 da suka rasu a dalilin cutar.

A nan Kano kuwa, ma’aikatar lafiya ta ce an yiwa mutane 6 gwajin cutar a jiya, sai dai ba’a sami ko da mutum guda mai dauke da cutar ba, abinda ke nuna cewa a yanzu jihar Kano na da sauran mutane 11 masu fama da cutar.

A jimlacce dai, an yiwa mutane dubu 47,595 gwajin cutar a nan Kano, cikin su kuma an tabbatar da cewa ta kama mutane dubu 1,740 guda 1,675 daga ciki sun warke sai guda 54 da suka rasu a dalilin cutar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!