Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yau Google ke cika shekaru 21 muhimman abubuwan da ya kamata ka sani game dashi

Published

on

Yau Google ke cika shekaru 21 muhimman abubuwan da ya kamata ka sani game dashi

Menene Google?

Google kamfanine na ‘yan kasar Amurka wanda ke hada-hadar kimiyyar yanar gizo-gizo wato intanet da Computer, Google yana baka dama ka binciki duk abinda kake so ka bincika a duk sanda kake so, shi kuma ya baka bayani akai, a hausance ana kiransa da “Matambayi Baya Bata”.

Tarihin Google:

Mr. Larry Page da Mr. Sergey Brin suka samar da Google a shekarar 1998 a lokacin da suke karatun digiri na uku wato PhD a jami’ar Stanford University dake Califonia.

Sakatariyar Google tana birnin California na kasar Amurka, izuwa shekara ta 2018 Google yana da ma’aikata guda Dubu Tamanin da Biyar da Hamsin (85,050).

Menene Google Account?

Google Account shine ka mallaki asusu (account) a kamfanin google wato dai kayi register dasu.

Meye Alakar Google Account da Gmail Account?

Da Gmail da Google Account duka abu daya ne idan ka mallaki Email din Gmail to shine dai Google account domin dukkansu na kamfani daya ne.

Google Sarki ne:

Tabbas Google Sarki ne shafin Google dake kan gaba a duniya yana da bangarori da dama birjik, wanda idan ka mallaki account dinsu to ka mallaki duka wadannan sai dai mutanen mu da yawa basu san wadannan bangarorin ba, zamu dauki wasu daga ciki masu muhimmanci ga al’umma muyi bayaninsu.

Gmail:

Shine email din Google wato gmail zai baka damar tura sako ko karbar sako ta intanet.

Play Store:

Idan kana da Google Account to ka mallaki account na Play Store ga masu Android Play Store shine inda zaka shiga domin yin downloading din manhaja a wayarka.

Google Search:

Matambayi Baya Bata, zai baka damar yin bincike a yanar gizo.

YouTube:

YouTube dandalin da zai baka damar kallo da kuma dora video a kai, Idan ka mallaki Google Account to ka mallaki account na YouTube domin shima YouTube mallakar kamfanin Google ne.

Google Plus:

Google Plus shi kuma daya ne daga cikin shafukan sada zumunta kamar facebook, twitter da sauransu, shima kuma mallakarsa shine ka mallaki account na Google, said ai a baya-bayan nan google sun rufe wannan sashe.

Blogger:

Da Google Account kana da damar bude blog wato shafin internet da zaka dinga ajiye bayananka.

Google Translator:

Google Translator zai baka damar ka dauki rubutu daga hausa ya mayar maka dashi turanci, ko kuma daga turanci zuwa hausa ko larabci, ko duk yaren da kake so ya koma. Sannan idan kana so har karanta maka zai iya yi cikin sauti.

Ka zabi wanda kake son ya karanta maka, tsoho, ko tsohuwa, yaro ko yarinya, mace ko namiji.

Google Map

Zai baka damar ganin ko ina kake a duniya da abubuwan da kake kusa dasu, misali ka je Abuja baka san sunan unguwar da kake ba, zaka iya shiga ka gani da ma sunan titin da kake, da kuma wuraren da suke kusa da wajen otel-otel, Restaurant, wato gidan abinci, ko kuma Schools, wato makarantu da sauransu.

Sannan zaka iya shiga ka duba cewa daga gari kaza zuwa kaza Mintuna nawa ne a jirgi ko a mota haka idan a kafa ne.

Google Alert:

Zai baka dama ka zabi kalmomi ko wasu bangare da kake so idan an samu sabon bayani akansa a internet to a sanar da kai ta email dinka.

Domin yin amfani dashi sai ka ziyarci www.alert.google.com

Google Chrome:

Browser ce da ke kan gaba a yanzu wadda kuma take da kariya, idan ka dora Gmail Account dinka akanta har password dinka da sauran bayananka duk zata dinga adana maka.

Google Drive

Zai baka damar ka adana bayananka akan yanar gizo.

Google Reverse:

Zai baka dama ka gano cikakken bayani akan hoto da kuma wanda ya fara dora hoton a internet.

Game Da Google Drive?

Google Drive wurin ajiye bayanai ne kamar dai Memory Card dinka, zaka iya ajiye bidiyo, sautin murya da ma hoto da kuma sauran kunshin bayanan ka akai, kamfanin google suka samar dashi a ranar 24 ga watan April na shekara ta 2012, ana iya mafani dashi a waya da kuma Computer.
Zaka iya saka wani file dinka akai sannan ka baiwa mutum link dinsa shima ya sauke ma’ana dai zaka iya turawa mutum wani file ta google drive.

Basheer Sharfadi

27-09-2019.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!