Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yau masu adaidaita sahu ke shiga yajin aiki a Kano

Published

on

Ƙungiyar muryar matuƙa baburan adaidaita sahu ta Kano ta ce, babu gudu ba ja da baya kan shirin ta na tsunduma yajin aiki a yau Litinin.

Mai magana da yawun ƙungiyar Malam Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Freedom Radio.

A cewar sa, za su tafi wannan yajin aiki ne domin nuna takaicin su kan irin wahalhalun da hukumar KAROTA ke ɗora musu.

Za a fara daure masu adaidaita sahu kan goyon gefe – KAROTA

Kano: An cafke ƴan adaidaitar sahun da suka shirya zanga-zanga

Ya kuma kara da cewa sun shirya yajin aikin ne don nunawa gwamnati irin muhimmancin da suke da shi, wajen kai ma’aikata guraren ayyukan su da kuma tafiyar da tattalin arziki.

A don haka ya bukaci masu sana’ar ta adai-daita sahu da su basu hadin kan da ya dace.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!