Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

A ranar Talata ne Sarkin musulmi ya cika shekaru 65 a Duniya

Published

on

A ranar Talata ne mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya cika shekaru 65 a duniya.

Sultan Abubakar III, wanda shi ne ɗan auta a cikin ƴaƴan marigayi Sarkin Musulmi Sir Saddiq Abubakar III, An haife shi ne a ranar 24 ga watan Agusta na shekarar 1956 a jihar Sokoto.

 

Alhaji Sa’ad Abubakar ya halarci Kwalejin Barewa da ke Zariya, daga nan kuma ya tafi Kwalejin horar da sojoji ta ƙasa wato NDA, a shekarar 1975.

Sarkin na cikin manyan hafsoshin sojin da aka yaye karo na 18 a kwalejin.

A watan Nuwamban shekarar 2006 ne, aka naɗa shi a matsayin Sarkin Musulmi.

Bayan rasuwar ɗan uwansa Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Macciɗo a hatsarin jirgin sama.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!