Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Freedom

Dimbin bashi ga kasashen Afrika koma baya ne gare su- Masana tattalin arziki

Published

on

Yayin da bashin da ake bin Nijeriya ya karu zuwa sama da Naira tiriliyan 46 a watan Disambar bara, Wani rahoton da BBC ta fitar ya bayyana cewa a shekarun baya-bayan nan kasar China ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen da ke samar da bashi ga ƙasashe masu tasowa.

Haka zalika binciken ya nuna cewa daga 2016 zuwa 2021, kasar China ta ba da rancen dala miliyan 185 ga ƙasashe 22 na Afrika.

Shugaban Bankin Duniya David Malpass, ‘ya bayyana damuwa kan basukan da China ke dumbuza wa ƙasashen Afirka masu tasowa’.

Wanda ya ce ‘kamata ya yi a riƙa bayyana ƙa’idojin yarjejeniyar irin wannan bashi kafin a bayar da shi’.

‘Wasu daga cikin cibiyoyin ba da rance na duniya, sun yi zargin cewa China na karɓar kadarorin da ba a yarda da su ba, a matsayin jingina kafin ba da rancen ‘.

‘Tare da  yin zargin cewa ƙasashen kan biya rancen a wasu lokuta ta hanyar sayar wa Chinar albarkatun ƙasar da suke da su’.

‘Sai dai kuma ita kasar China tana cewa tana ƙulla yarjejeniya da ƙasashen ne bisa tsarin dokokin duniya’.

Hakan tasa Freedom Radio ta tattauna da masanin sanin tattalin arziki na Jami’ar Bayero dake nan Kano Farfesa Ahmad Muhammad Tsauni da yace ‘’karbo bashin abune mai kyau, don bunkasar kasashe, tare da gudanar da ita kanta gwamnati, wanda bazata iya samar dashi ba da kanta sai ta nemi tallafi daga wasu kasashe’’.

‘’To sai dai kuma idan har bashin ya zamana ba’a bi ka’idojin da ya kamata abi ba wajen samar da su, babbar barazana ce ga kasar da ake bawa’’.

Wanda yace ‘’duba da cewa irin kasashen da basu da kyakyawan shugabanci, da cin hanci da rashawa yayi katutu, sannan kuma kasar da bata bin doka da oda, to shakka babu kasashe irin su China idan suna basu bashi, to zai zamana tare da kasar ake gudanar da mulkin wannan  kasar da aka dibgawa bashin’’.

A hannu guda Kuma Shima masani kan harkokin da suka shafi dangantaka tsakanin kasashe Farfesa Abubakar Jika Jiddere cewa yayi ‘‘Kowacce kasa tana bayar da bashi ne ba don tana so ba, ko don tana tausayin kasashen da suke bawa sai don wata bukatarsu, kama daga cin gajiyar ma’adanan da suke wannan kasar, don cin ma burin ta a bangaren tsaro da siyasa da kuma bunkasar tattalin arzikin kasarta’’.

Wanda ya ce ‘’kasashen da suka ci gaba suna jin dadin yadda suka jibgawa kasashe masu tasowa bashi, don a kaiga lokacin da baza su iya biya ba, wanda ba’a bada bashin sai kan sharuda masu karbi, inda daga kasar da ta bayar da bashin ita zata koma sarrafa kasar da ta bawa bashin, wanda hakan zai zamana kamar lokacin mulkin mallaka

Masanan dai sun tabbatar da cewa karbi bashi da kasashe keyi Abu ne Mai kyau, sai dai kuma ba’a bin hanyoyin daya kamata abi wajen amfani dasu, da a karshe yake jawowa kasar nakasu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!