Labarai
Yawan ciyo bashi ne ya tabarbara tattalin arziki kasar nan-DAG
Cibiyar wanzar da damokaradiya da cigaba al’umma DAAG ta bayyana cewa yawan ciwo bashi da gwmanatin jihar Kano ke yi ba zai haifar da mai ido ba.
Shugaban cibiyar Dr Muhammad Mustapha Yahaya ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a safiyar yau juma’a.
Yana mai cewa yawan ciyo bashin da gwamnatoci keyi ne yasa ake samun tabarbarewa tattalin arziki.
Yace a wani bincike da wasu kungiyoyi suka gudanar sun gano cewa, jihohi arewa su ciyo bashi da ya kai akalla Naira 1,221,147,361,723.62.
Inda jihar Kano ke da kaso mafi tsoka wajen ciyo bashi , da ya kai akala 78,054,829,156.67.
You must be logged in to post a comment Login