Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yawan dalibai a Kano ya sa muke dora azuzuwa a sama – Danlami Hayyo

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, cinkoson dalibai a makarantu ya sanya aka ta fito da tsarin yin azuzuwa masu hawa biyu zuwa uku.

Shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Dakta Danlami Hayyo ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio.

Shirin wanda ya yi duba kan manufar ba da ilimi kyauta kuma dole a Kano da kuma matsalolin da ke kewaye da hakan.

Ya ce jihar Kano na da dalibai sama da miliyan hudu wanda hakan ya tilastawa gwamnati fito da tsarin fadada wajen zama ga dalibai.

Allah ya albarkaci jihar Kano da yawan dalibai, kuma daliban sun yiwa azuzuwan da suke zaune kadan, sai  muka yi nazari muka gano cewa dora bene shi ne mafita ga matsalar” a cewar Hayyo.

Ko da yake batu kan tsarin daukan malamai na BESDA, Danlami hayyo ya ce “Malaman da suka samu shiga tsarin BESDA tun da farko an yi yarjejeniya kan wa’adin da za su yi, in kuma hali yayi za su iya samun aiki kai tsaye”.

Ya kuma ce, rashin gyaran azuzuwan makarantu da suka lalace, yana da nasaba da rashin kudi da gwamnati ke fama da shi a yanzu.

Muna da makarantu dubu bakwai a Kano, a kowacce makaranta idan za mu gyara aji guda daya za mu kashe Naira biliyan bakwai, to idan haka ne kuwa gaba daya gyaran zai kama Naira Biliyan Arba’in da tara, to ina gwamnati taga wannan kudi?” in ji Hayyo.

Danlami Hayyo ya ci gaba da cewa “Amma duk da haka gwamnati tana cire wani adadi daga kudin kananan hukumomi da kuma kudaden shiga da ake samu na jiha da kuma ribar yan kwangila duk dan a gyara azuzuwan dalibai a Kano.

Sai dai ya ce, gwamnati za ta ci gaba da kokarinta na ganin ta dore wajen bada ilimi kyauta kuma dole a Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!