Labarai
Yawan Fetur da ake samarwa a kullum ya ƙaru zuwa lita miliyan 71.5- MNDPRA

Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur ta kasa, NMDPRA ta bayyana cewa yawan man fetur da ake samarwa a kullum ya ƙaru zuwa lita miliyan 71.5 a watan Nuwambar bana, daga lita miliyan 46 a kullum da ake samu a watan Oktoba.
Hukumar ta ce gagarumin ƙarin a watan Nuwamba ya samo asali ne daga shigo da man da Kamfanin NNPCL ya yi, wanda ya samar da kashi 55 cikin 100 na wadataccen man fetur a kasuwannin kasar nan, daga hanyoyin cikin gida da kuma ƙasashen waje.
Takardar bayanai ta watan Nuwambar da aka fitar ta nuna cewa yawan amfani da man fetur a ƙasar nan ya ƙaru da kashi 44.5 cikin 100 zuwa lita miliyan 52.1 a kullum.
You must be logged in to post a comment Login