Labarai
Wadanda suka nemi N-Power sun kai miliyan 4
![](https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2020/07/5401f72f-hajia-sadiya.jpg)
Hukumar dake kula da ayyukan jin kai da kare Annoba ta kasa ta ce shafin ta na Internet da matasa sa za su nemi aikin yi na N-POWER kawo yanzu yawan wadanda suka nemi aikin ya fiye da miliyan 4.
Ministan Hajiya Sadiya Farouq ce ta sanar da hakan a shafin hukumar na twitter a daren jiya Lahadi.
Sanarwar ta kara da cewa ‘’Ni da abokan aiki na muna cigaba da kokarin muna tuntubar masu ruwa da tsaki don tabbatatar shirin ya samu nasara , bayan da aka kwashe kwanaki 16 da bude shafin ya zuwa yanzu masu sha’awar neman aiki a karkashin shirin ya kai miliyan 4.48”
Ma’aikatar dai ta bude shafin ta a ranar 26 ga watan Yunin da ya gabata.
You must be logged in to post a comment Login