Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yi hakuri kar ka sauya sheka daga PDP zuwa APC- Gwamnonin PDP ga Matawalle

Published

on

Wasu gwamnonin jam’iyyar PDP guda shida sun roki takwaransu na jihar Zamfara Bello Muhammed Matawalle da ya ci gaba da zama a jam’iyyar ta PDP maimakon canja sheka zuwa APC.

Gwamnonin sun hada da: Seyi Makinde na jihar Oyo, Nyeson Wike na Rivers, Bala Abdulkadir Muhammed na jihar BAUCHI, Darius Ishaku na Taraba, Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa da kuma Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto.

Gwamnonin na PDP dai sun kai ziyarar ce ga gwamna Matawalle a gidan gwamnatin jihar Zamfara da ke garin Gusau.

Da yak e jawabi yayin ganawa da gwamna Matawalle gwamnan jihar Rivers Nyeson Wike y ace bai san dalilin da ya sa ‘yan jam’iyyar APC ke zawarcin gwamnaonin PDP ba.

Saboda haka y ace akwai bukatar gwamnan ya yi watsi da bukatar APC na neman ya sauya sheka zuwa jam’iyyar.

Wannan na zuwa ne bayan wani makamancin wannan ziyara da gwamnonin jam’iyyar APC suka kai wa gwamna Matawalle.

Gwamnonin na APC sun hada da: Atiku Bagudu na Kebbi, Badaru Abubakar na Jigawa da kuma Mai Mala Bunin a jihar Yobe

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!