Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro: Daurarru sun yi yunkurin tserewa daga gidan gyaran dali da ke Bauchi

Published

on

Jami’an hukumar kula da gidan gyaran hali ta kasa da ke BAUCHI sun dakile wani yunkurin tserewa da wasu daurarru su ka yi a yau juma’a.

 

Rahotanni sun ce agajin gaggawa da jami’an tsaro da ke gadin gidan gyaran halin su kai, shi ya dakile yunkurin daurarrun na tserewa.

 

Shaidun gani da ido sun ce biyu daga cikin jami’an hukumar kula da gidan gyaran halin sun jikkata.

 

Al’ummomin da ke makwabtaka da gidan gyaran halin dai sun ce sun yi ta jin karar harbin bindiga wanda ya faru da misalin karfe goma sha biyu na rana, kafin sallar juma’a.

 

Mai magana da yawun hukumar kula da gidan gyaran halin a jihar BAUCHI Abubakar Algwallary, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!