Connect with us

Labarai

Yusuf Ali Abdallah ya zama PRO na 1 a ƙungiyar masu gabatar da shirye-shiryen al’umma a Redio

Published

on

Ƙungiyar masu gabatar da shirye-shiryen al’umma a kafafen yaɗa labarai na Redio sun zaɓi Yusuf Ali Abdallaha a matsayin jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar.

Hakan na cikin wasiƙar kama aiki da ƙungiyar ta gabatar ga Yusuf Ali Abdallah mai dauke da sa hannun shugabanta Sani Abdurrazak Darma.

A cikin wasiƙar, ƙungiyar ta yi la’akari da yadda Yusuf ke bada gudunmawa wajen ciyar da harkokin aikin jarida gaba.

Sanna kuma yana da jajircewa wajen bunƙasa harkokin jama’a musaman ma idan ya shafi ayyukan sa.

Ƙungiyar ta buƙace shi da yayi aiki tuƙuru wajen ciyar da ita gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!