Labarai
Zaɓen 2023: INEC ta sanar da ranar zaɓen shugaban ƙasa da gwamnoni
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta ayyana 25 ga watan Fabrairun 2023 a matsayin ranar zaɓen shugaban ƙasa.
Shugaban hukumar na Farfesa Mahmud Yakubu ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja ranar Asabar.
Farfesa Yakubu ya ce a yanzu za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar Asabar 25 ga Fabrairun 2023, yayin da za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisun jihohi a ranar 11 ga Maris ɗin 2023.
Farfesa Yakubu ya bayyana cewa tsayar da ranar akan lokaci zai ba ba da damar yin shirye-shirye a kan lokaci daidai da tanade-tanaden dokokin zaɓe wadda ta ce, a bada sanarwar zaɓe akalla kwanaki 260 kafin zaɓen.
Shugaban na INEC ya kuma ce za a sanar da ƙa’idojin zaɓen a nan gaba Kaɗan.
#Solacebace
You must be logged in to post a comment Login