Labarai
Zaɓen Anambara: Ƴar manuniya ce ga ci gaban Najeriya – Dakta Dukawa
Masanin siyasar nan a jami’ar Bayero da ke kano Dakta Sai’du Ahmad Dukawa ya ce zaben da aka yi wa Farfesa Charles Soludo matsayin gwamnan jihar Anambra yana nuni da cewa yan Najeriya na da yancin shiga harkar siyasa su kuma nemi mukaman da suke so.
Dakta Sai’du Ahmad Dukawa ya bayyana hakan a zantawar sa da Freedom Rediyo kan batun zaben jihar ta Anambra.
“Hakan na nuni da cewa masu ilimi mai zurfi suna shiga harkar siyasa kuma a dama da su hakan zai kawowa kasa ci gaba sabanin wadanda basu da ilimin komai sai dai kawai su shiga harkar siyasar kai tsaye”.
A ranar Larabar nan ne hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa ta ayyana Farfesa Charles Soludo na jamiyar APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar ta Anambra.
A cewar mai gabatar da sakamakon zaɓen Farfesa Florence Obi, tace, Farfesa Charles Soludo ya sami yawan kuri’u da ake buƙata wanda hakan ne ya bashi nasarar lashe zaɓen geamnan Anambra.
Zaɓaɓɓen gwamnan wanda tsohon gwamnan babban bankin ƙasa ne ya samu nasarar bayan kammala zaɓen da aka gudanar a ranar Talata.
Charles Soludo ya samu ƙuri’un da ake buƙata daga ƙananan hukumomi 19 cikin 21 da ake da su a jihar.
Yawan ƙuri’un sun kai 112, 229 bayan da aka kammala kidayar na ƙaramar Hukumar Ihiala.
Nasarar dai na zuwa ne bayan da ya kayar da abokan hamayyar sa na jam’iyyar PDP Valentine Ozigbo mai kuri’u 53,807 da kuma Andy Uba na jam’iyar APC wanda ya sami ƙuri’u 43,285, sai kuma Ifeanyi Uba na Jamiyar YPP daya sami ƙuri’u 21, 261.
You must be logged in to post a comment Login