Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Sharhi

Sharhi: Idan ‘yan siyasar ƙasar nan ba su bi a hankali ba, za su sanya ƙasar cikin hatsarin siyasa – Farfesa Kamilu Fagge.

Published

on

Masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero da ke nan Kano,  ya bayyana cewa idan har ‘yan siyasar Najeriya ba su yi taka tsan-tsan ba to kuwa za su iya sanya kasar cikin hatsarin siyasa.

Farfesa Kamilu Sani Fagge ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Freedom Radio.

Fagge ya ce, wannan Mataki da ko wanne bangare na kasar ya dauka ya nuna shirin fara tunkarar zaben shekarar 2023 mai zuwa.

“Yadda alkiblar kasar ta nuna a yanzu ya nuna cewa, duka bangarorin Najeriya sun shirya tunkarar zabukan 2023,”

“Idan ya kasance kowanne bangare ya ja zare lallai sai dan takarar shubagan kasa ya fito daga yankinsa hakan  yayi nuni da yadda siyasar Najeriya ke samun armashi,”

“Hatsarin kuma shine muddin wasu suka fara nuna wariya da nuna kabilanci da kuma rikicin  addini shakka babu wannan ya nuna kasar ba ta koyi darasi daga abin da suka faru a baya na fadace-fadace da hakan yayi sanadiyyar tarwatsewar mulkin dimokuradiyya” a cewar Farfesa Kamilu Fagge.

Wannna dai na zuwa ne bayan da aka jiwo kungiyar dattawan arewacin Najeriya na  bayyana cewa babu wanda zai tilasta wa al`ummar yankinta zabar wani dan takarar shugaban kasa da ya fito daga kudancin kasar a zaben shekarar 2023.

Kamar yadda kakakin kungiyar Dakta Hakeem Baba Ahmed ya shaida wa BBC cewa yankin  arewa nada  yawan masu zabe, don haka ‘yankin ba ya shakkar ko wace irin barazana.

Haka zalika shima  tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha an jiyo shi na  goyon bayan gwamnonin kudancin Najeriya  kan batun mayar da kujerar shugaban kasa yankin.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!