Labarai
Za a ci gaba da rigakafin zazzabin cizon sauro – Ganduje
Gwamnatin jihar Kano ta ce zata ci gaba da yaki da zazzabin cizon sauro a karshen kowanne wata har zuwa watan Oktoban shekarar da muke ciki.
Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan ta cikiin wata sanarwar da ma’aikatar ta fitar mai dauke da sa hannun jami’ar yada labaran ma’aikatar Hadiza Namadi.
Ta cikin sanarwar Kwamishinan ya kuma yabawa ma’aikatan lafiya da duk wanda suka yi aikin rabon maganin na kwanaki hudu da aka kammala a Juma’ar nan.
Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce za’a kuma a cigaba da shirin gudanar da rabon maganin zazzabin cizon sauro a kwanaki hudun kowanne wata don tabbatar da an inganta lafiyar al’ummar jihar Kano musamman kananan yara.
You must be logged in to post a comment Login