Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za a ci gaba da rigakafin zazzabin cizon sauro – Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce zata ci gaba da yaki da zazzabin cizon sauro a karshen kowanne wata har zuwa watan Oktoban shekarar da muke ciki.

Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan ta cikiin wata sanarwar da ma’aikatar ta fitar mai dauke da sa hannun jami’ar yada labaran ma’aikatar Hadiza Namadi.

Ta cikin sanarwar Kwamishinan ya kuma yabawa ma’aikatan lafiya da duk wanda suka yi aikin rabon maganin na kwanaki hudu da aka kammala a Juma’ar nan.

Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce za’a kuma a cigaba da  shirin gudanar da rabon maganin zazzabin cizon sauro a kwanaki hudun kowanne wata don tabbatar da an inganta lafiyar al’ummar jihar Kano musamman kananan yara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!