Labarai
Za a dauki ‘yan sandan sarauniya guda dubu 3,850 a jihar Zamfara
Rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara ta amince da daukar mutane 3,850 ‘yan asalin jihar domin horas da su a matsayin ‘yan sandan sarauniya wato constabulary, domin tallafawa jami’an tsaro wajen yaki da bata-gari a fadin jihar.
Mai magana da yawun rundunar SP Shehu Muhammad ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar yau a birnin Gusau.
SP Shehu Muahammad ya ce wadanda za a baiwa horon suna cikin mutane 7,500 da babban sufeton ‘yan sanda Muhammed Adamu ya amince a dauka a matsayin ‘yan sandan sarauniya na musamman a fadin jihar.
Sanarwar ta kara da cewa an tantance mutanen a matsayin wadanda suka dace a karo na farko, da za su je kwalejin horas da ‘yan sanda dake jihar Sokoto na tsawon watanni biyu.
Sannnan kuma ta bukaci wanda suka cike fom din neman gurbin ‘yan sandan sarauniya da su duba sunayensu a ofisoshin ‘yan sanda dake yankunansu ko kuma sakatariyar karamar hukumarsu, domin ko za a fara horon daga ranar 9 ga watan da muke ciki na oktoba.
You must be logged in to post a comment Login