Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

NACA – Akwai bukatar kashe naira dubu 50 ga duk mutum guda mai dauke da HIV a kowacce shekara

Published

on

Hukumar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta kasa NACA ta ce tana bukatar kashe kudi naira dubu hamsin ga duk wani mai fama da cutar a shekara guda.

Shugaban hukumar Dr Gambo Aliyu ne ya bayyana hakan yayin zantawa da jaridar Daily Trust a Abuja.

Dr Gambo Aliyu ya ce hukumar tana wani aikin hadin gwiwa tare da sauran masu ruwa da tsaki wajen ganin sun kafa wani asusun tallafawa masu fama da cuta mai karya garkuwar jiki a kasar nan.

Ya kara da cewa alkaluman da suke hannunsu sun nuna cewa akwai masu dauke da wannan cuta sama da miliyan guda a kasar nan, kuma sun dogara ne da tallafin da suke samu daga kungiyoyin kasashen waje, kuma da zarar sun daina tallafawa za a shiga cikin gagarumar matsala.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!