Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za a fara dawo da ƴan Najeriya da suka yi hijira zuwa Nijar gida

Published

on

Gwamnatin jihar Borno ta fara shirin dawo da ƴan jiharta da ke gudun hijira a jamhuriyyar Nijar.

Gwamnatin jihar ta aika da tawagar jami’anta zuwa garin Diffa, domin shirya tsarin da za a bi wajen fara jigilar ƴan gudun hijirar zuwa gida.

Yayin ziyarar Kwamishinan gina gidaje da sake tsugunar da ƴan gudun hijra na jihar Borno Injiniya Mustapha Gubio ya shaidawa Freedom Radio cewa nan bada jimawa ba aikin zai kankama.

Ya ce, “Tuni aka fara gyaran matsugunnan su wanda yanzu haka ana dab da kammalawa, sannan a fara mayar da su”.

Wani mazauni yankin da bai bayyana sunansa ba, ya ce, yayi farin ciki matuƙa da ganin an fara shirin mayar da su gida bayan da ya shafe shekara bakwai yana gudun hijira”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!