Labarai
Za a rika tuna Buhari a matsayin tsayayyen shugaba da ya hidimta wa Najeriya- A U

Ƙungiyar Tarayyar Afirka A U, ta aike da saƙon ta’aziyya bisa rasuwar tsohon shugaban Kasa Muhammadu Buhari ga iyalansa da gwamnati bayan mutuwar tsohon shugaban a jiya Lahadi.
Ƙungiyar ta ce za a rika tuna marigayi Buhari a matsayin mutum mai ɗabi’u na gari kuma tsayayyen shugaba, wanda ya hidimta wa Najeriya da alfahari,” a cewar shugaban tarayyar ta African Union Mahmoud Ali Youssouf ta cikin wata sanarwa.
Ya ƙarra da cewa “a baki ɗayan mulkin marigayi Buhari, ya kasance mai kishin Afirka, mai kishin haɗin kai da shugabanci na gari”.
You must be logged in to post a comment Login