Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Za a samar da cibiyoyi 12 na masu fama da cutar Daji a kasar nan – Buhari

Published

on

Gwamnatin tarayya ta amince da kafa sababbin cibiyoyin kula da masu fama da cutar daji a wasu asibitoci goma sha biyu da ke sassa daban-daban na kasar nan.

 

Ministan lafiya Osagie Ehanire ne ya bayyana hakan a wani bangare na bikin ranar masu fama da cutar ta daji ta duniya da ake gudanarwa ranar 04 ga watan Fabrairun kowacce shekara.

 

Ya ce samar da wadanda sababbin cibiyoyi zai taimaka wajen rage kaso hamsin cikin dari na kudade da masu fama da cutar ke kashewa.

 

Ministan ya ce gwamnatin ta sanya sabbin na’urorin kula da masu fama da cutar daji a asibitocin koyarwa na jami’ar Nigeria da ke Nsukka dana Benin da Sokoto da Ibadan dana Shika da ke Zari’a da sauran wasu asibitocin da dama.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!