Labarai
Za a samar da tashoshin manyan motoci a titin Kano zuwa Abuja – Fashola
Majalisar zartarwa ta kasa (FEC) a jiya laraba ta amince da sake fasalta aikin titin Kano zuwa Abuja.
Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola ne ya bayyana haka bayan kammala taron majalisar zartarwa ta kasa.
‘‘Na gabatar da mukalu da dama a yayin taron wanda daya daga ciki shine aikin sabunta kwantiragin da aka bayar a baya na kwaskwarimar titin Kano zuwa Abuja.’’
“A baya dai kwaskwarimar titin aka bayar kawai amma yanzu cikakken aiki za ayi inda za a sake aikin titin baki daya ta kowane bangare.”
“Majalisar zartarwar ta amince da bukatar da muka gabatar na neman sauya fasalin aikin wanda a baya aka tsara za ayi akan naira biliyan dari da hamsin da yanzu kuma an mai da shi naira biliyan dari bakwai da casa’in da bakwai da miliyan dari biyu da talatin da shida” acewar Fashola.
A sabon aikin bayan gina sabon titi da fadada shi za a kuma gina tashohsin manyan motocin dakon kaya da kuma samar da wuraren awun kaya da toll gates da kuma wasu kananan hanyoyi na gefen titi tsakanin jihohin Kano, Kaduna, Niger da kuma birnin tarayya Abuja.
You must be logged in to post a comment Login