Connect with us

Coronavirus

Za a sassauta dokar zirga-zirga gobe Alhamis a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta sassauta dokar hana zirga zirga daga gobe alhamis karfe 6 na safe zuwa 12 Daren gobe.

Mataimakin Gwamnan Kano Dr Nasir Yusuf Gawuna ne ya bayyana hakan yau lokacin taron manema labarai akan halin da ake ciki akan cutar Corona.

Ya kuma yi kira ga alumma da suyi amfani da wannan lokaci na azumin Ramadan domin yin adduar Samun saukin cutar ta Corona

Ya kuma ce a gobe ne Gwamna zai kaddamar da rabon kayan rage radadin zaman gida a masarautar Kano

Wakiliyar mu ta fadar Gwamnatin Kano Zahrau Nasir ta ruwaito cewa kwamishinan harkokin adddini Dr. Muhd Tahir Adam na cewa bayan ganawa da malamai daga kowanne bangare an amince ba zaa a gudanar da sallar tuhajjudu da tarawih da tafsir ba sai dai Gwamnati zata dauki nauyin tafsiran a gidajen rediyo.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!