Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Za a yi gwanjon Motar Diego Maradona

Published

on

Rahotanni dake fitowa daga kasar Spain na cewa za a yi gwanjon Motar Kawa (Luxurious), ta marigayi tsohon gwarzon dan wasan kasar Argentina Diego Maradona.

Motar, wacce take kirar Porsche 911, marigayi Maradona ya yi amfani da ita ne a karshen kakar wasanninsa a nahiyar Turai, a shekarar 1992, lokacin da ya ke wasa a kungiyar kwallon kafa ta Seville.

“Tabbas Motar za ta yi daraja sosai fiye da kudin da aka saka na yin gwanjon ta”.

“Bugu da kari za ta dau hankalin mutane da dama ciki har da ‘yan Kwallo kasancewar ta ta dan wasa Maradona ” inji Gregory Tuytens, kwararre kan gwanjon motoci a kasar Belgium .

An saka motar a kasuwa, a tallan kafar Intanet (Online), a kan Kudi Euro dubu 240, 800, daga Larabar nan zuwa ranar 10 ga Maris.

Motar ta shafe shekaru 20, a hannun wanda ya mallake ta dan kasar Andalus (Spain), da yake tsibirin Majorca, kafin a sake sayar da ita ga ‘yan kasar Faransa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!