Labarai
Za a yi jana’izar Shiekh Dahiru Bauchi gobe Juma’a

A gobe Juma’a ne ake sa ran za a gudanar da jana’izar marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu da Asubahin yau Alhamis.
Rahotonni sun bayyaa cewa, za a yi jana’ira shehun malamin ne a gidansa da ke Kofar Gombe a cikin garin Bauchi.
Fitaccen Malamin wanda ya yi fama da jinya ya kuma kasance wanda ya bayar da gudummawa sosai wajen ci gaban addinin Musulunci a fadin nahiyar Afrika.
Malamin wanda ya kasance jagoran darikar Tijjaniyya na tsawon lokaci, ya rasu ya bar mata huɗu, ‘ya’ya da jikoki sama da ɗari.
You must be logged in to post a comment Login