Labarai
Za a yi mamakon Ruwan sama a makon gobe- NiMet

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet ta yi hasashen samun tsawa da ruwan sama daga yau Lahadi zuwa ranar Talata a fadin kasa.
Hasashen yanayin da NiMet din ta fitar a ranar Asabar a Abuja ya bayyana cewa, za yi tsawa a safiyar ranar Lahadi tare da ruwan sama matsakaici a wasu sassan Taraba da Adamawa a yankin Arewa.
A cewar rahoton da hukumar ta fitar, ana sa ran za a yi tsawa a sassan jihohin Filato da Kwara da Nasarawa sai Neja da Kogi da Binnuwai
A yankin kudu, ana sa ran samun ruwan sama a sassan jihohin Oyo da Ogun da Ondo da Ebonyi sai Ekiti da Edo da Abia da Imo da Enugu da Anambra sai Lagos da Akwa Ibom da Cross River da kuma Rivers, hasashen ya nuna za a yi ruwan sama a mafi yawan sassan yankin da kuma budewar rana.
A ranar Talata, kuma, a yankin Arewa, ana sa ran cewa da safe za a samun yanayin tsawa tare da matsakaicin ruwan sama a sassan jihohin Zamfara da Kaduna.
Haka kuma ta kara da cewa, za a yi tsawa da ruwan sama a sassan jihohin Taraba da Kaduna da Adamawa da Zamfara, sai Kano da Bauchi da Gombe da kuma jihar Borno.
A yankin Arewa ta tsakiya ana hasashen tsawa da ruwan sama a wasu sassan jihohin Neja da Filato da Benuwai da safe.
You must be logged in to post a comment Login