Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Za koma kwallo a gasar kasar China a watan Yuli

Published

on

 

Hukumar kwallon kafar kasar Sin (China ) ta zabi biranen Sozhou da Dalian a matsayin biranen da za a fara gasar wasannin kakar kwallon kafar kasar da aka shirya farawa watanni biyar baya.

Gasar tun da fari an shirya zata gudana a watan Fabrairun bana , sai dai ta samu tsaiko sakamakon Annobar Corona , wanda yanzu haka an saka ranar 25 ga watan Yuli na komowa gasar.

Labarai masu alaka.

Za’a dawo gasar wasan Tennis ta US Open a bana ba tare da ƴan kallo ba

Kuskure ne babba dawowa kwallon kafa yanzu-Gianni Infantino

A wata sanarwa da hukumar kwallon kafar ta China (CFA) ta fitar a shafin ta na Internet , tace gasar ta China (CSL) , za ta dawo cikin matakan kariya daga cutar da za’a dauka wanda a baya an dakatar da gasar ne don lafiyar yan wasa da bunkasa gasar.

Gasar kungiyar Guangzhou wacce tsohon dan wasan kasar Italiya Fabio Cannavaro ke jagoranta ita ke rike da gasar wacce zata kare kambun data dauka a shekarar bara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!