Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Jigawa

‘Yan sanda sun cafke dan fashi a Jigawa

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wani dan fashi a yankin karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa, wanda ake zargin yana da hannu dumu-dumu wajen aikata wannan mummunan ta’ada.

A kwanakin baya ne dai jamin’an ‘yan sanda dake ofishin su na Fanisau a jihar ta Jigawa, suka karbi korafin wani matashi mai suna Abbas Ibrahim wanda yace an yi masa fashi, a ranar 30 ga watan 6 na wannan shekara yayin da yake kan hanyar sa ta zuwa kauyen Jidawa a yankin karamar hukumar Dutse.

Mai korafin yace wani mutum ne dauke da kokara da kuma adda ya tare shi ya yi masa fashin kudin dake gurin sa gaba kidaya.

Karin labarai:

Amfani da fasahar zamani zai taimaka wajen magance matsalar tsaro -Dakta Sani Lawan Malumfashi

‘yan sanda a jihar Bauchi sun kashe wasu ‘yan fashi

Akan haka ne jami’an ‘yan sanda suka kaddamar da bincike ya yin da suka sami nasarar cafke wani matashi mai suna Zubairu Abashe mai shekaru 22, dan kauyen Kabulle a karamar hukumar Dutse, inda nan take ya tabbatar da cewa yana daga daga cikin wandanda suka aikita laifin ba tare da bata lokaci ba, yana mai jaddada cewa dukkan fashin da ake aikatawa a wannan yanki yana da hannu.

Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa SP Abdu Jinjiri yace zuwa yanzu suna cigaba da tatsar bayanai daga gurin dan fashin, inda daga nan za su kamo sauran abokan sa dake taya bera bari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!