ilimi
Za mu ɗaga likafar Kwalejin sa’adatu rimi zuwa jami’a -Ganduje
Gwamnatin jihar Kano za ta amsa kiran da kwalejin Sa’adatu Rimi ke yi na ɗaga likkafarta zuwa jami’a.
Gwamnan Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan lokacin da kwamitin gudanarwar kwalejin suka kai masa ziyara.
Gwanduje ya ce zai bada haɗin kai wajen ɗaga likkafar kwalejin tare da da haɗa kai da Hukumar kula da jami’o’i a ƙasar nan NUC.
“Abin alfahari ne matuƙa a ce kwalejin ta zama cibiyar bayar da Digiri, kuma kira na anan shi ne a inganta harkokin koyo da koyarwa”.
“Abin farin cikin bai wuce yadda za a ɗaga likkafar kwalejin ba tare da an kashe kuɗaɗe ba
domin yawancin kayayyakin aikin da ake buƙata akwai su a kwalejin” in ji Ganduje.
Wannan dai na zuwa ne yayin da shugaban kwalejin Farfesa Yahaya Isa Bunkure ya jagoranci tawagar, tare da roƙom gwamnan kan batun ɗaga likkafar kwalejin zuwa jami’a, da kuma sanar da shi cikar kwalejin shekara 40 da kafuwa.
You must be logged in to post a comment Login