Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu biya wa ɗaliban da suka yi karatun lauya kudi zuwa makarantar koyon aikin- Kabiru Getso Haruna

Published

on

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta sanar da shirin bayar da tallafin karatu na musamman ga ƴan asalin jihar da suka yi karatun lauya amma ba su je makarantar koyon aikin lauya ba.

Shugaban hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Kano, Alhaji Kabiru Haruna Getso ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da ƴan jarida a ofishinsa, a wani ɓangare na bikin cika shekara guda da gudanar da mulkin gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ya bayyana matsayin jihar Kano a matsayin jiha ta gaba wajen bayar da tallafin karatu ga ƴan kasa kamar yadda gwamnatin tarayya ta amince da ita.

Bugu da kari, Alhaji Kabiru Haruna Getso ya bayyana cewa an zabo jihar Kano ne domin gudanar da wani taron kwanaki biyar da ya hada manyan masu ruwa da tsaki a fannin bayar da tallafin karatu don magance muhimman batutuwan da suka shafi wannan fanni.

Ya kuma yi kira ga ƴan asalin Kano da ke karatun shari’a a duk duniya da su tuntubi hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar kano don samun dama, kamar biya musu kuɗaɗen ci gaba da karatu kamar yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauki nauyin biyan kudin karatu.

Haka kuma ya yaba da nasarorin da gwamnatin jihar ta samu wajen daukar nauyin ƴan asalin Kano don samun digiri na biyu a duniya ta hanyar bayar da tallafin karatu.

Ya kuma jaddada irin ɗimbin alfanu da aka samu wajen bayar da tallafin karatu na ƙasashen waje da kuma na cikin gida, inda ya bayyana cewa shirin tallafin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi na bayar da tallafin karatu ya zama na farko a tarihin jihar Kano.

Alhaji Kabiru Haruna Getso ya yi karin haske kan jita jitar da ake ya ɗawa kan masu karatu a ƙasar India na cewa suna cikin mawuyacin hali inda yace abin da ake yaɗawa bashi da tushe da balle makama illa kawai ana so a shigo da siyasa ne a ciki.

Haka kuma ya taya Gwamna Abba Kabir Yusuf da Mataimakinsa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo murnar nasarar da suka samu na tsawon shekara daya a kan karagar mulki, inda ya jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaban ilimi da kuma ci gaban al’umma a Jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!