Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan Nijeriya za su shiga mawuyacin hali matukar aka ci gaba da yajin aiki- Minista

Published

on

Gwamnatin tarayya, ta bayyana cewa, al’ummar kasar nan za su shiga cikin mawuyacin hali matukar kungiyar kwadago ta kasa NLC ta dage a kan bakanta na yajin aiki.

Ministar kwadago Nkeiruka Onyejeocha, ce ta bayyana hakan ta cikin shirin gidan Talabijin na Channels.

Haka kuma ta ce, a shirye gwamnatin tarayya ta ke wajen ganin cewa ta samu daidaito tsakaninta da kungiyoyin kwadago, don haka za su ci gaba da tattaunawa da kungiyar.

Minista Nkeiruka Onyejeocha, ta kuma ce, kawo yanzu yajin aikin ya janyo tsaiko a fannoni da dama musamman ma ilimi inda hakan ya janyo wa dalibai gaza samun damar rubuta jarrabawa sakamakon rashin samun ababen hawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!