Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu dakatar da albashin ma’aikatan kungiyar SSANU – Buhari

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar dakatar da albashin ma’aikatan da ba malamai ba da ke jami’o’in kasar nan sakamakon tsunduma yajin aikin da ba shi da dalili.

 

Ministan kwadago da samar da aikin yi Chris Ngige ne ya bayana hakan yayin zaman tattaunawa da kungiyoyin da ke yajin aikin.

 

Ya ce sashi na 43 na dokar kungiyar kwadago na shekarar 2004 ta bai wa  gwamnati damar dakatar da albashin ma’aikata a lokacin da suke yajin aiki.

 

Sai dai ya gargade su da cewa, gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen mutunta dokoki na tsarin kungiya musamman wajen kiran kungiyoyin don tattaunawa.

 

Ngige ya ce yajin aikin da kungiyar ta SSANU da NASU ke yi, ya sabawa dokokin kungiyar kwadago taa Najeriya.

 

Kungiyoyin biyu  sun fara yajin aiki na ba-sani-ba-sabo a ranar 5 ga Fabrairu, 2021 a kan gazawar gwamnatin tarayya wajen warware matsalolin su na rashin biyansu albashi da ya kai Naira Biliyan 40, da sauran bukatu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!