Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za a kammala hanyar Abuja Kaduna zuwa Kano kafin 2023 – Buhari

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce za a kammala aikin sake gina hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano a cikin zangon farko na shekarar 2023.

 

Karamin Ministan Ayyuka da Gidaje Aliyu Abubakar ne ya bayyana hakan a a jiya Alhamis yayin da yake duba bangare na uku na aikin daga Zariya zuwa Kano.

 

Ya ce kammala aikin hanyar, na daya daga cikin abubuwan da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta bai wa fifiko a yanzu.

 

A cewarsa, saboda muhimmantar da aikin hanyar, ministan ayyuka da gidaje Babatunde Raji-Fashola ya ziyarci wajen da ake gudanar da aikin tare da tawaga ta musamman, inda kuma wasu Injiniyoyi suka ziyarci aikin don kara tantancewa.

 

Aliyu Abubakar ya kuma ce, jajircewar na a matakin ganin an kammala aikin kafin karshen gwamnatin shugaba Buhari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!