Labarai
Za mu dauki mataki kan masu daukar nauyin masu fadan Daba- Gwamna Abba Kabir

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir yusuf ya ce, gwmnatinsa za ta hada kai da jami’an tsaro domin daukar mataki kan yan siyasa da ake zargi da daukar nauyin matasan da ke aikata kaifukan fadan daba da kwacen waya a jihar kano.
Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne ta cikin jawabin da ya gabatar a daren ranar laraba a gidan gwamnati jim kadan bayan dawowarsa daga kasa mai tsarki bayan gudanar da aikin Hajjin bana.
Gwamnan ya kuma ce shirye-shirye sun yi nisa wajen samar da tsarin koyar da sana’o’i ga matasan a wani mataki na yaki da zaman banza da ya addabi da matasan da ake zargi.
Wakilin Freedom Radio a gidan gwamnatin Kano Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewa gwamnan ya kuma yi alkawarin tattauwana da shugabannin kasuwar waya ta Farm Center wadda ibtila’in gobara ya shafa, domin sake gina sabbin shaguna da basu jari domin rage musu radadin asarar da ta same su.
You must be logged in to post a comment Login