Connect with us

Labarai

Za mu fara yi wa yan Kasuwar Kauye Rijista- Hukumar CPC

Published

on

Hukumar kare hakkin masu sayen kayayyaki ta jihar Kano watau Kano Consumer Protection Council, ta ce, zata fara yi wa yan kasuwar da ke gudanar da sana’o’insu a kasuwannin kauye rijista domin tabbatar da ingancin kayyakin da suke sayarwa da kuma cika mudu.

 

Jami’ar hukumar mai kula da shiyar Kano ta Arewa Hajiya Sadiya Umar Bichi, ce ta bayyana hakan lokacin da ta jagoranci kai ziyara kasuwar Dawanau da kuma ta Badume a Larabar makon nan.

 

Ta ce, hukumar ta kai ziyarar gani da ido ne kan yadda wasu kamfanoni ke gudanar da ayyukan su da kuma jin matsalolin da suke fuskanta su da abokan kasuwancin su.

 

Jami’ar ta kara da cewa ziyarar za ta taimaka wajen dakile korafe-korafen da masu sayen kayayyaki ke kai wa hukumar da kuma zaburar da yan kasuwar domin inganta kayan su.

 

Yayin ziyarar, masu kamfanonin da hukumar ta ziyarta sun bayyana jin dadin su da kuma tabbatar da bayarda goyon bayansu ga wannan hukumar.

Da yake jawabi bayan kammala zagayen Jami’in hukumar kare hakin mai saye da mai sayarwa a kasuwar Dawanau Alhaji Ahmad Isah, ya ce, zagayen da aka yi a bangarorin kasuwar zai taimaka wajen kara tsaftace kasuwar tasu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!