Labarai
Za mu gaggauta kawo karshen matsalar rashin tsaro a jihar Kano – Gwamna Abba Kabir Yusuf

Gwamnatin jihar kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce za ta yi duk mai yuwa wajen dakile duk wata barazana ta rashin tsaro a fadin jihar musamman yankunan ƙananan hukumomin Tsanyawa da Shanono da a yanzu ke fama da hare-haren ƴan ta’adda.
Gwamnan jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar jaje da ya kai garuruwan Yankamaye, Bisirawa, Masaurari da Sundu a ƙaramar hukumar Tsanyawa, sai Faruruwa dake Shanono inda ‘yan bindiga suka kai hare-hare a kwanakin baya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro domin taimakawa wajen cafke miyagun da suke addabar yankuna.
You must be logged in to post a comment Login