ilimi
Za mu gina dakunan karatu (Library) 110 a makarantun firamare – Gwamnan Gombe
Gwamnatin jihar Gombe za ta kashe naira miliyan dari uku da talatin da uku don gina dakunan karatu (LIBRARIES) a makarantu daban-daban da ke fadin jihar.
Gwamnan jihar ta Gombe Inuwa Yahaya ne ya bayyana haka lokacin da ya ke kaddamar da sabon dakin karatu na zamani da gwamnati ta gina a makarantar firamaren Jekadafari, da kuma rabon babura da kayyyakin wasanni da na koyarwa a makarantar.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na gwamnan jihar ta Gombe Ismaila Uba Misilli, ta ce, gwamnan wanda sakataren gwamnatin jihar farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ya wakilta, ya ce, gwamnatin sa ta gaji tarin matsaloli a bangaren ilimi, wadda ita ce a matsayin jiha ta talatin da hudu cikin jihohin kasar nan talatin da shida inda bangaren na ilimi ya samu koma baya.
‘‘Tun da muka zo abin da muka fara shine nazartar bangarori da ke bukatar agajin gaggawa sakamakon sakaci da aka yi da su a baya, hakan tasa muka ayyana dokar ta baci kan bangaren ilimi’’
‘‘Samar da dakunan karatu (Libraries) a makarantun firamare daya ne daga cikin dabarun da muke ganin zai taimaka wajen dakile wasu matsaloli a bangaren ilimi’’
‘‘Saboda haka na umarci shugabannin makarantun firamare da sakatarorin ilimi da su ware wasu lokuta da zai kai akalla mintuna tamanin a duk mako ga daliban firamare don su rika zuwa dakunan karatu’’ a cewar Inuwa Yahaya.
Tun farko da ya ke gabatar da jawabi kwamishinan ilimi na jihar ta Gombe Dauda Batari Zumbuk, ya ce, daukin gaggawa da gwamnatin Inuwa Yahaya ke yi ga bangaren ilimi a jihar zai taimaka gaya wajen bunkasa harkokin ilimi a jihar
You must be logged in to post a comment Login