Labarai
Za mu gyara titunan da suka lalace a sanadin damuna – Ganduje
Gwamnatin jihar Kano tace zata gyara titunan jihar Kano da suka lalace musamman ma sanadiyyar damuna.
Manajan darakatan hukumar kula da gyaren titunan Idris Wada Sale Dawakin tofa Kano ne ya bayyana hakan a yau ya yin da yake zantawa da manema labarai.
Ya Kara da cewa a yanzu haka daga titunan da suka lalace sun yi nasarar gyara guda 18 ya yin da kuma suke kokarin cigaba da gyara wasu 13 nan ba da jimawa ba
Ya Kara da cewa duba da yadda gwamnati ta damu kan lalacewar wasu titunan ne yasa gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya umarce su da Fara gyare-gyaren tun daga lokacin damuna.
Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa daga titunan 13 da za’a fara gyaran su nan ba da jimawa ba, sun hada da titin da ya taso daga kofar Naisa zuwa kwanar Diso da Titin Tafawa Balewa da titin Sharada , da titin Ibrahim taiwo da sauran su.
You must be logged in to post a comment Login