Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu toshe Layukan dogo na tashoshin jiragen kasa a Kano – KARMA

Published

on

Gwamnatin jihar kano ta ce za ta gyara tituna goma sha shida a wasu sassan jihar, baya ga toshe wasu daga cikin layukan dogo wandanda mahada ce da wasu titunan.

Shugaban hukumar kula da gyaran titunan jihar Kano KARMA Injiniya Idris Wada Sale ne ya bayyana hakan, ta cikin shirin ’’Barka da hantsi’’ na nan tashar freedom radio, wanda ya maida da hankali kan halin da wasu titunan jihar Kano ke ciki.

Idris Wada Sale ya kara da cewa, al’umma na taka rawa wajen lalacewar tituna ta hanyar zuba shara a magudanan ruwa wanda hakan ke sanadin lalacewar titinan.

Wada Idris ya kuma ce, manyan motoci na taka rawa wajen kara lalata titunan a sassan jihar Kano.

Shugaban hukumar ya bukaci al’umma da su bada hadin kai a duk lokacin da ma’aikatan gyaran titin suke gudanar da ayyuka su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!